Sa’an nan kuma ya kasance daga wadanda suka yi imani ,kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri, kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi.Wadannan ne ma’abuta albarka. (Surat al-Balad: 17-18)
Kamar yadda aka bayyana a cikin ayah ta sama ,Allah (swt) ya umarci bayin sa (su tausaya wa juna )saboda su sami rahmar sa, tare da shiga aljannah da samun saukin wajen hisabi. Bayin Allah (swt)da suka sadaukar da rayuwar su wajen neman yardar Allah(swt), su kanyi kokari wajen bin umarnin Allah(swt). Kyakkyawar Imanin su da Allah(swt) yasa suka fahimci muhimmancin Tausayi da Rahma,kuma suna da yakinin cewa ba abinda zai faru sai da sanin Allah. Kuma sun gane muhimmancin tausayi da Rahmar ubangiji da yayi masu.kamar yadda aka sani masu imani suna da tunani da natsuwa,sanin haka yasa suka zama wayayyu a cikin al’umma,kuma suka tabbata masu tausayi a cikin jama’ar musulmi.
A binda bayin Allah nagari suka zaba wa kansu a wannan al’amari, shine nuna wa juna tausayi da sauran jama’a, wanda zai jawo hadin kai da farinciki ga rayuwar al’umma duniya da lahira.Wasu lokuta kauna da tausayi da bayin Allah nagari ke nunawa al’umma yakan jawo masu matsala da zargi da wasu al’amura na wahalar da kai. ,(an-nafs).Kuma suna shan wahala wajen fuskantar marasa gaskiya ta wajen nuna masu hanyar kwarai tare da jawo hankalinsu su bar aikata haramun. Wannan shine gaskiyar tausaya wa juna, saboda kauce wa barna da illar sa,kuma suna kokarin koyar da halin kwarai ta yadda za’a fahimci yadda Allah (SWT) ya koyar a cikin Alkur’ani maigirma, wajen kare shi daga aikata aikin da zai kai shi ga shiga wuta, kuma ba za’a bashi daman dawowa duniya ba ya gyara aikin sa.A bisa wannan dalili bayin Allah nagari suke karfafa mutane da su aikata aiki nagari wanda zai sa su samu yardan Allah da tausayin sa, tare da samun Rahmar ubangiji shine shiga gidan Aljannah.Kamata mutum ya sani cewa aikata mugunta bazata kai mutum ga samun rahmar Allah (SWT) ba,kuma aika ta kuskure bisa ganganci yana jawo fushin Allah (SWT) da azaba.A bisa wannan dalili ,bayin Allah magari suke bin koyarwar Manzon tsira Muhammad (SAW) da halayen sa wanda Alkur’ani maigirma ya bayyana mana.’’Kuma, lalle ,hakika kana a kan halayen kirki,manya". (Surat al-Qalam: 4)