Babban dalilin samun rarraba a tsakanin musulmi a tsawon shekaru da kuma irin tashin hankali da zaluncin da a ke wa musulmi a sassan duniya daban daban, shi ne cewa wasu musulmin sun dauka rike sallah kadai da azumi da zuwa hajji sun ishe su addini, don haka ba ruwansu da al’amuran da ke da bukatar mika wuya da sadaukarwa domin ba abin da ya dame su kamar holewa da jin dadin rayuwar ni’ima da suke ciki, ba sa ko tunani game da matsalolin da ‘yan uwansu musulmi suke fuskanta a sassan duniya.

Musulmi mutane ne masu tsarkin zuciya da kyakkyawan tunani. Daya daga cikin halayen musulmi shine ba sa kallon sauran mutane ta mahangar jinsi ko al’ada, ko matsayin mutum a cikin al’umma ko kuma kowane irin ma’aunin bambanci na duniya. Allah ne kadai ya san matsayin kowane mutum ta fuskar takawa, imani da kuma kusancinsa ga Allah mahalicci. Don haka Allah ya haramta wa muminai masu imani yin maganganu sabanin haka. Don mutumin da ya ce “Na yi imani” to ya zama lalle mu kyautata zato a gareshi tare da taimako da karfafarsa a duk lokacin da yake bukatar hakan.
“Muminai maza da muminai mata mataimakan juna ne. Suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani da mummuna, sannan suna tsaida sallah, da bada zakka kuma suna bin umarnin Allah da manzonSa. Wadannan Allah zai yi musu rahama. Allah mabuwayi ne, mai hikima.” (Sura Tauba, aya ta 71)
“Kafirai mataimakan juna ne. In ba ku aikata ba fitina za ta afku a bayan kasa da barna mai yawa.” (Suratul Anfal, aya ta 73)

Musulmi a musulunci cike suke da shu’urin soyayya, da aminci inda suke zaune cikin fahimta da son juna. Duk al’ummar da ke da irin wadannan dabi’u ta fi saurin habaka da samun ci gaba. Har ila yau, wani babban abu shine wadanda ke kokari tare da karfafa hadin kai da son juna Allah ya yi musu alkawarin taimako da karfafawa. Shi ya sa a ayoyi da dama na Alkur’ani Allah ya ke gaya musu kada su rarraba, in suka yi haka sai karfinsu ya tafi kuma rauni ya mamaye su. Daya daga cikin ayoyin ita ce:
“Ku bi Allah da ManzonSa kuma kada ku yi jayayya a junanku sai ku tarwatse karfinku ya tafi. Ku yi hakuri. Allah yana tare da masu hakuri.” (Suratul Anfal, aya ta 46)

“Wadannan suna rigengeto zuwa ga alhairai, kuma za su tarar da su. Ba ma dora wa rai sai abin da za ta iya. A gurinmu akwai littafi wanda yake furuci da gaskiya. Su ba za a zalunce su ba.” (Suratul Mu’minun, aya ta 61 – 62).

“Ya ku wadanda suka yi imani idan kun fita zuwa yaki a tafarkin Allah to ku bambance. Kada ku ce da wanda ya zo muku a musulmi ‘Kai ba mumini ba ne’ saboda kwadayin samun duniya. Allah a wajensa akwai ganima mai yawa. Kamar haka ku ka kasance a baya amma Allah ya yi muku tagomashi. Saboda haka ku bambance. Allah yana sane da abin da ku ke aikatawa.” (Suratun Nisa, aya ta 94)
“Matsala ta uku ita ce yadda musulmi ke suka da cin naman ‘yan uwansu. Matan kuwa su kan taru a gidajensu da sunan wani lamarin addini, amma sai su buge da gulma; wance ta yi kaza, su wane sun yi kaza... A maimakon bata lokaci a kan wadannan gumace gulmacce, me zai hana su yi tunanin kalubalantar zindikancin masu ra’ayin Darwin da ýan akidar zahiranci (materialists)? Ko su rika ilmantar da juna kan sha’anin addini da ya shafi imani, tsoro da kuma son Allah. Amma don me wasu musulmi za su taru suna cin naman ‘yan uwansu musulmi? Misali, akwai wani majalisi da a ka yi a wani wuri, inda bayan an karanta littafin Risalat Nur sai kuma a ka shiga gulma da zunde. Ba na ce kowa ne ke yin hakan ba, amma dai da dama haka a ke yi. Ba wanda ke son a rika yi da shi bayan idonsa. To in haka ne meye amfanin gulma, in banda hali ne na mutanen banza. Bai kamata mutane su rika cin naman junansu ba; zai fi kyau su so juna tare da girmama juna, ta haka ne Allah zai taimake su. Su kasance masu fadin “Ya Allah, ka haskaka duniya da haskenka, ka gaggauto da tabbatar musulunci a duniya, ya Allah a cikin wannan karni.” Irin addu’o’in da ya kamata su rika yi kenan don neman taimakon Allah da daukinsa. Shin a baya ka taba ji ana maganar soke bizar shiga kasashe ko batun hadin kan duniyar musulmi? Amma yanzu akwai muhimman ci gaba da a ka samu musamman wajen yunkurin kafa cibiyar hadin kan musulmi ta Turkiya. Lokacin da na fara magana kan wannan al’amari kimanin shekaru biyu da suka gabata, mutane sun yi ta mamakin abin da na ke fada, saboda ba su taba zaton haka ba. In da za ka duba jaridun wancan lokaci, za ka ga ba wani abu da suka buga game da wannan al ;amari don kuwa da niyya suka ki bugawa. Amma abubuwa sun canja yanzu.” (An dauko daga hirar Adnan Oktar a tashar Gaziantep Olay ranar 30 ga Janairu, 2010.)