RUDUN JUYIN HALITTA

DOWNLOAD THE BOOK

Download (DOC)
Comments

CHAPTERS OF THE BOOK

< <
22 / total: 22
RUDUN JUYIN HALITTA
Rushewar Kimiyyar Darwiniyanci Da Tushen Akidojinsa

 


BABI NA 20

Tarurrukan SRF:
Shirye-shirye don fadakar da Mutane Akan Juyin Halitta

Farfagandar juyin halitta, wadda ta samu makararriyar karbuwa, wani tarnaki ne ga imani da kyawawan dabi'u na cibiyar binciken kimiyya (Science Research foundation) SRF, wadda take sane da irin wadannan kutungwila, ta kuduri naiyar sanar da jama'ar kasar Turkiyya akan gaskiyar al'amarin ta fuskar kimiyya.


Taron Farko - A Istanbul

Daya daga jerin taruurukan kasa da kasa da suka shirya wato cibiyar binciken kimiyya (SRF)itace wadda akak gabatar a shekara ta 1998. Mai taken "Rushewar ka'idar juyin halitta: Hujja akan yin halitta", an yi tane a Istanbul ranar 4 ga Afrilu, 1998. Taron, wanda ya samu gagarumar nasara, ya samu halartar kwararrun sanannun duniya kuma suka samar da wata hanya wadda a karon farko aka saka ka'idar juyin halitta akan sikelin tambaya kuma suka rushe shi a kimiyance, a kasar turkey. Mutane daga kowane sako na al'ummar Turkawa sun halarci taron, kuma ya fa'idantar. Wadanda basu samu wurin zama a dakin tarn ba sun kalla ta akwatinan talabijin da aka sanya a waje.

Taron ya samu halartar sanannun masana daga kasar Turkey da kasashen waje. Bayanan da shugabannin SRF suka gabatar wanda ya bayyana irirn kudurin dake kunshe a ka’idar juyin halitta, said a SRF ta gabatar da wani faifan bidiyon data shirya.

Dr. Duane gish da Dr Kenneth Cumming, sanannun masana kimiyaar duniya ne na cibiyar binciken rayuwa da burbushin halittu. Sun bayyana hujjoji cewa ka’idar juyin halitta bata da wani ginshiki. A wannan taro ne, daya daga cikin masana kimiyya a wannan zamani a kasar Turkey, Dr. Cevat Babuna ya nuna irin mu’jizar dake tattare a halittar dan Adam.


Taro na Biyu – Istanbul

Taro na biyu a jerin taruurukan kasa da kasa shine wanda aka gabatar watanni uku bayan na farko a watan Juli 5, 1998 a Cemal Resit Rey Conference Hall har ila yau a Istanbul. Masu jawabai – shida Amurkawa daya dan kasar Turkey sun gabatar da jawabai akan yadda kimiyyar zamani ta rushe Darwiniyanci. Dakin taro na Cemal Resit Ray Conference Hall, mai daukar mutum dubu ya cika da masu sauraro.

A takaice, jawaban taron ya kunshi abubuwa kamar haka;

Farfesa Micheal P. Girgouard: A jawabinsa yake cewa, “Shin zai yiwu ace rayuwa ta samu ta hanyar kicibis?”, Micheal Girouard, farfesa a fanning limin rayuwar halittu a jami’ar Louisiana ta kud, yayi bayani tare da bada misalai akan faduwar sunadaran gina jiki, sashen rayuwa, kuma ya cika jawabinsa akan cewa zasu iya samuwa ne kadai ta hanyar wannan kwararren mai kera halitta.

Dr Edward Boudreaux: A jawabinsa, mai taken “Adon dake cikin sunadarai”, Edward Boudereaux, farfesa a fannin sunadarai na jami’ar New Orleans, ya gabatar da cewa lallai wasu sunadarai sun jeru ne don rayuwa ta wanzu.Farfesa carl fliermans: Sanannen masanin kimiyya a kasar Amurka kuma farfesa a fannin kwayoyin halittu a jami’ar Indiana day a gabatar da wani bincike akan “yinkuirn canza sunadara ta hanar kwayoyin halitta” wanda ya sami tallafi daga ma’aikatar tsaron amurka, Carl fliermans ya rusa da’awar masana juyin halitta a fanninsa na kwayoyin halittu.

Farfesa Edip keha: Farfesa a fannin binciken sunadaran halittu, Edip Keha, shi kadai ne dan kasar Turkey mai jawabi a taron. Ya gabatar da bayanai akan kwayar komayya kuma ya karfafa ta hanayr gabatar da shaidun da suke nuna yadda kwayar halitta ta samu daga kwararren makerin halitta.

Farfesa David Menton: shima farfesa ne a fanning binciken tsarin halitta daga jami’ar Washinfton, David Menton, a jawabisa wanda yake dauke da kayataccen gwajin day a nuna a na’ura mai kwakwalwa, yayi nazari akan bambancin tsarin halittar fuka-fukan tsuntsaye dana halittu masu rarrafe aban kasa, wanda ya haifar da sakamakon karyata cewa wai tsuntsaye asalinsu daga dabbobi ne masu rarrafe.

Farfesa Duane Gish: shahararren masanin juyin halitta, a jawabinsa mai taken “Asalin Mutum”, farfesa Gish, ya karyata rubuce-rubucen da aka yi akan cewa wai mutum asalinsa daga gwaggwon biri ne.

Farfesa John Morris: shagaban cibiyar binciken halitta (ICR) kuma sananne a fanning binciken kasa, ya gabatar da jawabi akan akidoji da falsafar dake tattare a juyin halitta. Ya kara fadada jawabi da cewa wannan ka’ida an canza tana don ta zama ta addini kuma masu kare ta sunyi imani da Darwiniyanci tare da mummunan kudurinsu akan addinin gaskiya.

FLIERMANS

PROF.DUANE GISH

PROF.DAVID MENTON

PROF. EDWARD
BOUDREAUX

Masu sauraro, bayan an kammala jawabai, sun fahimci cewa juyin halitta wata akida ce ta karya wadda kimiyya ta rushe a kowane mataki. Haka kuma, faya-fayen da aka nuna da taken “Rushewar ka’idar juyin halitta:

Hujjoji akan halitta” wanda cibiyar binciken kimiyya ta haske a dakin taro na CFR conference Hall yaja hankalin mutane tare da kayatar dasu. Faifen ya kunshi hotuna 35, kowane daya yana nuni izuwa da’awar juyin halitta ko shaida akan halitta.


Taro Na Uku-Ankara

Taro na uku a jerin tarurrukan kasa da kasa an gabatar dashi ne a rnar 12 ga watan juli, 1998 a Shearaton Hotel dake Ankara. Masu jawabi-uku Amurkawa da Baturke daya-sun gabatar da hujjoji da shaidu wadanda suke nuna cewar kimiyyar zamani ta rushe Darwiniyanci.

Koda yake dakin taron dake Ankara Sheraton Hotel an gina shi don ya dauki zaman mutum dubu ne, amma mahalarta taron sun zarce mutum 2,500. sai aka sanya akwatinan talabijin a wajen dakin taron ga wadanda basu samu wurin zama ba. Faifan majigin da aka haska mai taken “Rushewar ka’idar juyin halitta: Hujjoji akan halitta” a kusa da dakin taron shima yaja hankalin mutane. A karshen taron, jama’a suka mike suna tafi ga masu jawabin, wanda yake nuna yadda jama’a suke ilmantuwa akan hujjojin kimiyya dake rushe rudun juyin halitta da tabbatar da hujjojin halitta

Ganin irin nasarorin da wadannan tarurruka suka haifar yasa cibiyar binciken kimiyya SRF ta fara shirya irin wadannan tarurruka a ko’ina a fadin kasar Turkey. Tsakanin watan Agusta na 1998 zuwa watan Mayu na 1999, an gabatar da tarurruka sittin 60 a birane daban-daban. SRF ta cigaba da gabatar da tarurrukanta wurare daban-daban a fadin kasar.

Tsarki ya tabbata a gareka!
Babu sani a garemu face
Abinda Ka sanar damu, lalle ne
Kai, Kai ne Masani Mai hikima.
(Surat al-Baqara, 32)

 
   
    
22 / total 22
About this site | Make your homepage | Add to favorites | RSS Feed
All materials can be copied, printed and distributed by referring to this site.
(c) All publication rights of the personal photos of Mr. Adnan Oktar that are present in our website and in all other Harun Yahya works belong to Global Publication Ltd. Co. They cannot be used or published without prior consent even if used partially.
© 1994 Harun Yahya. www.harunyahya.com - info@harunyahya.com
page_top