A rayuwar bil – adama mutane suna ganin tasirin hikimar Allah ta irin baiwar daya sanya a kwakwalensu. Wannan kuwa wasu maganadison sadarwa ne da ke da ke isarwa da tara bayanai a zuciyar Dan-adam. Kuma koda yake akwai irin wannan al’amari na baiwa a zahirance, mutane kan lura ne kawai da wadanda aka sanya musu cikin kakwalensu. Don haka, a bisa tsarin Allah mai hikima, halayyarmu ta zahiri ta kasance fassarar abin da yake boye cikin kwakwalenmu ne, kuma muna fahimtar duk wadannan abubuwa da ruhin da Allah ya sanya mana; wato ta hanyar gain, da ji, da kuma tabawa da fahimtar su.(Allah) wanda ya halicci dukkan abu ya kyautata halittarsa, kuma ya fari halittar mutum daga yunbu (tabo). Sannan ya sanya asalinsa daga wulakantaccen ruwa da aka fitar; sannan ya siffanta shi, ya busa masa rai daga ruhinsa, kuma ya sanya muku ji da gani da zuciya (tunani). Kadan ne ku ke godewa! (Sura Sajda, aya 7 – 9)
An baiwa bil-adama kwakwalwa da ta tattara komai da komai na bayanai da ilmuka. A hankali, mataki mataki, Allah ya ke gina tunani da sanya bayanai a kwakwalen mutane, kuma yana ci gaba da sabunta kaifin tunani da ingancin kwakwalen nasu a tsawon rayuwar kowannensu. Misali, yanzu ga shi kana karanta wannan bayani, kuma nan da ‘yan mintuna abin da ka karanta zai sami gurbin zama a cikin kwakwalwarka (kamar rikoda). Zai kuma ci gaba da kasancewa cikinta na tsawon kwanaki, ko watanni ko kuma na tsawon shekaru ma (ya danganta da karfin hardar kwakwalwarka) inda za ka rika tuno shi daga lokaci zuwa lokaci. Duk lokacin da ka yi amfani da baiwarka ta tunani za ka iya tuno al’amura masu yawan gaske da ke dankare a cikin kwakwalwarka. Wadannan al’amura kuwa sun hada da muhimmai da wadanda ma ba su da muhimmanci ko girma sosai, wadanda kuma ba su kirguwa. Misali, duk da shudewar shekaru masu yawan gaske, amma har yanzu ka kan iya tuno ranar farko da ka fara zuwa makaranta a rayuwarka; ta irin wasannin da ku ka rinka yi da abokanka, da kuma irin farin cikin da ka dinga yi a waccan rana muhimmiya, duk yana nan daram a kwakwalwarka. Wannan kundin bayanai da ke cikin kwakwalwarka zai ci gaba da kasancewa tare da kai har ranar da rayuwarka ta kare. Mutane, wadanda Allah ya halicci ruhi kuma ya sanya a jikinsu, sai suka dauka mallakar wannan ruhi a gare su kamar su ne suka kage shi da kansu, wanda kuma wannan babban kuskure ne. Duk yayin da suka tuno da wani al’amari a rayuwarsu, lokacin da za ka ji sun ce “Na yi farin ciki a waccan rana,” “Na yi matukar murna da annashuwa a waccan rana,”su kan yi zaton ikonsu ne ba ikon Allah ba ne ya sa suka iya tuno wa da lamarin.